A cewar rahoton Kamfanin Dillacin Labaran Hauza, an gudanar da shirye-shirye da dama a wannan zama na ma'abota addini, da nufin taya Manzon Allah (SAWA) da Ahlul Bait (AS) juyayin mummunar masifa ta shahadar Imam Husaini (AS) da sahabbansa amintattu a filin Karbala.
A farkon zaman, an gudanar da taron ɗaga tutar juyayin da ke ɗauke da sunan "Qamaru Bani Hasheem; Hazrat Abul Fadlil Abbas (AS)" wanda matasan Abul Fadlul Abbas suka aiwatar. Bayan haka, mahalarta sun gabatar da taron latmah da dukan kirji, inda mawakin Ahlul Bait, "M. Shamsu Fuddiyya" ya jagoranci rera wakokin juyayin. Haka kuma, an gabatar da 'yar takaitacciyar wasan kwaikwayo ta tamsiliyya akan abubuwan da suka faru a Ashura, wanda hakan na daya daga cikin shirye-shiryen ranar farko ta wannan makoki.
Wannan zama ya gudana ne a ƙarkashin kulawa da jawabin "Sheikh Sunusi Abdulƙadir", wakilin 'yan uwa na garin Kano. A cikin jawabinsa, bayan yin tsokaci kan shigar sabuwar shekarar Musulunci, ya yi bayani kan ayyuka da ladubban da suka kamata a gudanar a farkon watan Muharram.
Sheikh Dr. Sunusi Abdulƙadir, a wani bangare na jawabinsa, ya jaddada muhimmancin neman yafiyar Allah (istigfari), neman yafiyar mutane da kuma biyan basussukan da ake bin mutum.
A karshe, ya yi takaitaccen bayani kan bangarori na juyin juya halin Ashura na har abada da kuma muhimmancin raya ambato da sadaukarwar Imam Husaini (AS) a cikin wannan wata ga masu juyayin.







Ra'ayinka